SiyasaJamus
Tanzaniya ta karbi alluran rigakafin corona
July 25, 2021Talla
Alluran da yawansu ya kai miliyan guda, kamfanin Johnson & Johnson ne ya samar da su.
Dama dai Tanzaniyar na daga cikin kalilan na kasashen Afirka da ba su karbi alluran ko ma fara rigakafin cutar ta corona ba.
Kasar ba ta yi hakan ba ne tun da fari saboda cijewar da marigayi shugaban kasar John Magufuli wanda ya mutu cikin watan Maris ya yi, cewa addu'o'i kadai sun isa maganin corona.
Sabuwar kasar ta yanzu, Samia Suluhu Hassan, ta sauya wannan tunani ta kuma amince da duk wani abu da kimiyya ta tabbatar game da cutar.