Tarihin hambarren Shugaba Mohamed Mursi na Masar
May 5, 2015Mohammad Muammad Mursi Isal Ayyat, hambarraren shugaban Masar,wanda a yanzu yake zaman daurin shekaru 20 a jarum, kan laifin ziga magoya bayansa tayar da tarzoma yayin da yake kan mulki, an haiffe shi a garin Adwa da ke Jihar Sharkiya a shekarar 1951, wato yanzu yana da shekaru kusan 64 ke nan.
Ya samu shaidar gama digiridinsa na farko a jami'ar birnin Alkahira a tsangayar kimiya da fasaha, kana bayan shekaru uku ya sake samun shaidar gama karatun digiri na biyu a jami'ar a bangaren kera na'urorin 'yan sama jannati, kafin ya zarce zuwa jami'ar California da ke Amirka yadda ya samu digirin-digirgin ya kuma koyar na yan shekaru, kafin ya dawo kasarsa ta Masar ya ci gaba da koyarwa a jami'oin Alkahira da Zaqaziq kai harma da jami'ar Fath da ke Libiya.
Mursi ya shiga kungiyar 'Yan Uwa Musulmai a shekarar 1979, yadda ya rike makami a ofishinta na siyasa. Ya zama dan majalisa har sau biyu, a shekarun 1995 da kuma 2000, yadda ya samu shaidar zama dan majalisa mafi gabatar da koke da bin kadin mutanansa a duniya.
A shekara ta 2010 ya jagoranci kafa wata gamayyar kungiyoyin masu fafutukar neman sauyi su 20 da kuma kawancen tabbatar da demokiradiyya a Masar da ya kunshi kungiyoyi 40, cikinsu har da kungiyar Mohammad Barade.
A shekarar 2011, bayan da kungiyar 'Yan Uwa Musulmai ta kafa jam'iya mai suna Alhuriyya wal adala, wato yanci da adalci, an zabi Mursi a matsayin shugaban jam'iyyar da ta yanke shawarar tsai da Khairatil Shatir a matsayin dan takarar shugaban kasa, kamar yadda Mursi din yake fadi a wancan lokacin.
Daga baya hukumar zabe ta ki amincewa da takarar Khairat Shatir karkashin jam'iyyar ta Yan Uwa Musulmai a yayin da ya rage 'yan kwanaki a rufe sayar da tarkardun shiga takara, lamarin da ya kai ga tsayar da Mohamed Mursi a matsayin dan takarar kungiyar.
Kafin ya zama shuagaban kasar, an taba daure shi har sau biyu, na farko daurin watanni 7 a shekarar 2005, bayan da ya shiga zanga-zangar nuna adawa da korar wasu alkalai da aka yi, wadanda su kai zargin tafka magudi a zaban shugaban kasar wannan shekarar. Dauri na biyu kuma, shi ne a ranar da aka fara zanga-zangar neman shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus, yadda bayan mako daya ya fice, shi da sauran firsinoni daga gidan yarin, sakamakon batar layar da jami'an tsaro su kai a gidajen yaruka dama kan titunan kasar wata ranar juma'ar da 'yan kasar suka kira zanga-zanga. A ranar Mursi ya bayyana a dandalin Tahreer, yadda ya kara tayar da tsimin masu zaman dirshan.
Bayan da ya kara da 'yan takara 12, ya zo kan gaba a zagayen farko, yadda a zagaye na biyu ya kayar da abokin takararsa, Ahmad shafiq da karamar tazara.
Tun a ranar da aka rantsar da Mursi a matsayin zabbbaen shugaban kasar ta Masar na farko da aka zaba kan tafarkin demokiradiyya, ya yi wa 'yan kasar da suka zaku da ganin sauyi alkawarin girka mulkin adalci da 'yanci gami da kyautatuwar rayuwa.
Shekara guda da Mursi din ya yi kan mulki, ya kasa tsinana wani abun azo a gani, a bangarorin tsaro da tattalin arziki. Wasu na dora alhakin haka kan rashin kwarewarsa da kungiyarsa ta 'Yan Uwa Musulmai wadanda ba su taba rike madafan iko a tsawan shekaru 80 da kafuwarsu. A yayin da wasu ke dora hakan ga kutunguilar da sojojin kasar suka kitsa masa.
An kifar da gwamnatin Mursi a watan Yulin shekara ta 2013.