1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

110511 Porträt Fußballer Cisse

May 18, 2011

Cisse ya zama ɗan wasan Afirka mafi nuna bajinta cikin 'yan wasan ƙwallon ƙafa a Jamus.

https://p.dw.com/p/11IrA

Burin da kowane ɗan wasan ƙwallon kafa a nahiyar Afirka ke son cimma shi ne watan wata rana a wayi - gari ya zama mai samun kuɗi mai yawa, kuma ɗan wasa Papiss Demba Cisse, wanda ɗan asalin ƙasar Senegal ne dake buga wasa anan Jamus ya sami wannan nasarar, daga kasancewar ɗan wasa akan titi ya zuwa ga ɗan Afirka daya fi zura ƙwallo a tarihin Jamus harma ƙungiyar ƙwallon ƙafar daya ke bugawa wasa ta Freiburg tana masa murnar zama ɗan wasan daya fi jefa ƙwallaye a raga a cikin ƙungiyar, wanda kuma ya ɗaga darajar sa har sai huɗu - idan an kwatanta da yanda ƙungiyar ta saye shi tunda farko, kuma duk da wannan bajintar bai mayar da kansa a matsayin mai girman kai ba.

Shi dai Pappis Demba Cisse yana da kamanni biyu ne. Na farko, idan ya shiga filin wasa, to, kuwa yana nuna halin ba sani ba sabo ne, amma idan ba'a fagen wasa ba ne, to kuwa shi mutum ne mai jin kunya sosai, kuma bai cika yin magana ba musamman bisa la'akari da irin sa'ar daya samu a rayuwa.

Cisse, ɗan ƙasar Senegal ne mai shekaru 25 da haihuwa, ya kai ƙololuwar matsayin da matasa 'yan wasan Afirka da dama ke son kaiwa na buga wasa a manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya, domin kuwa ƙwallaye 25 daya zura a kakar wasan bana sun mayar dashi zama ɗan wasan Afirka daya fi samun nasara a Jamus, kana ɗan wasan daya bunƙasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafar SC Freiburg:

Fußball Bundesliga SC Freiburg und 1. FC Nürnberg Papiss Cisse
Hoto: AP

" Cisse yace Hakan yasa ni alfahari da farin ciki, harma zan fi yanda nake yanzu haka ƙoƙari. Haka nake yi idan na shiga fili har ya zuwa lokacin tashi domin cin ƙwallo."

Tarihin wasansa a Jamus

'Yan wasan ƙungiyar SC Freiburg da Cisse ke bugawa wasa sun bayyyana shi a matsayin mutumin daya ɗauki salon yanda Jamusawa suke son mutum ya yi aikin sa, domin in ya shiga fili yakan yi iya ƙoƙarin sa a wasan, harma idan ma'aikatan sashen kula da lafiya na ƙungiyar suka ce kar yayi wasa, ba ya jin daɗi kuma wannan ɗabi'ar ce ta kai shi nesa. A kakar bana shi ne mutum na biyu daya fi cin ƙwallo bayan Mario Gomez. Cisses ya tuna yanda ya fara buga wasa:

" Kamar sauran 'yan wasa a ƙasar Senegal, akan titi na koyi ƙwallon ƙafa na, wanda ke nufin kai ne zaka koyawa kanka da kanka, tunda wasan ƙwallo akan titi bashi da wani tsari, duk abinda ya zo maka ne za ka yi."

Farashin sa a fagen Wasa

Cisse ya ƙara samun sa'a ne bayan da wani mai bayar da horo -ɗan kasar Faransa ya kai shi ƙungiyar ƙwallon Mates dake Faransar, inda ya sanya hannu akan ƙwangilar buga wasa a rukuni na biyu. Ba tare da wani ɓata lokaci ne ba kuma likkafar sa ta yi gaba a yayin wasa tsakanin ƙungiyar Mates da kuma Freiburg, inda aka gano cewar shi fitaccen ɗan wasa ne, kuma ƙungiyar Freiburg ta saye shi akan kuɗi Euro miliyan ɗaya da dubu 500. Ko da shike a wancan lokacin magoya bayan ƙungiyar freiburg sun nuna adawar su ga wannan farashin bisa hujjar cewar ya yi tsada ƙwarai, amma a yanzun nan da ake batu farashin ɗan wasan zai kai na kuɗi Euro miliyan 15. To ko yaya Cisse yake ji da wannan shahara tasa:

Kombobild Fußball Eintracht Frankfurt Theofanis Gekas Freiburg Papiss Cisse
Hoto: AP/DW Grafik

" Sana'ar wasan ƙwallo ba mai sauƙi bace. Mutane suna zaton abune mai sauƙi idan suka ga kana tuƙa mota mai tsada kuma kana kuɗi mai yawa, amma sana'a ce mai wahala, wadda idan baka mayar da hankali ba kuma baka da ƙarfin yinsa, to kuwa ba za ka cimma burin ka ba.

Cisse dai ya cimma burin sa tunda manyan ƙungiyoyi ƙwallon ƙafa irin su Arsenal da Liverpool dake Ingila suna ta zawarcin sa, kana ƙungiyar Freiburg ma tana fatan zai ci gaba da zama cikinta, amma ya fi ƙaunar buga wasan Premier na Ingila.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Umaru Aliyu