Tarihin Yahouza Sadissou Madobi
August 27, 2013An haifi Yahouza Sadissou Madobi a shekarar 1966 a garin Madobi dake cikin Jamhuriyar Nijar. Kuma ya shafe shekaru kimanin 10 yana aiki a nan Sashen Hausa na DW.
Tsohon malamin makaranta ne. Ya zama dan majalisa cikin Jamhuriya ta Shida, kafin sojoji su kifar da gwamnatin a shekara ta 2010.
Ranar Talata 13 ga watan Agusta 2013 aka bayyana Yahouza Sadissou Madobi a matsayin Minsitan Sadarwa da hulda tsakanin hukumomin gwamnatin Nijar, a cikin sabuwar gwamnatin kasar da ta kunshi ministoci 36, karkashin Firaminista Briji Rafini.
Sai a saurari sautin da ke tare da wannan rubutu, domin jin cikakken hira da Yahouza bisa tarihinsa, wuraren da ya yi makaranta, da aiyuka kafin ya zama minista.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal