1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro a kan rikicin yankin Kosovo

November 5, 2007
https://p.dw.com/p/C14v

Nan gaba a yau ne, za a koma tebrin shawarwari a birnin Vienna,na ƙasar Austriyya, a game da rikicin yankin Kossovo,tsakanin Sabiyawa da Albaniyawa, bisa shiga tsakanin rukunin ƙasashe 3 masu bin dinddigin wannan rikici, wato Amirika,Russie, da Ƙungiyar Tarayya Turai.

Wannan taro ya biwo bayan wani makamancinsa, wanda a ka shirya a watan da ya gabata ba tare da cimma nasara ba,to saidai a wannan karo, ɓangarorin dabam-dabam na kyauttata zaton a samu masalahar warware wannan taƙƙadama.

A farko Wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia ya gabatar da wani pasali na samar da ɗan ƙwarƙwaryan yancin kai ga yankin Kossovo bisa kular Majalisar Ɗinkin Dunia, to saidai Albaniya tare da ɗaurin gidin Russie, ta yi watsi da wannan shriri.