1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen Afrika a Senegal a game da batun sappara miyagun ƙwayoyi da ta´adanci

September 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuA4

Ƙasashen 23 na yankuna yama da tsakiyar Afrika, sun kawo ƙarshen taro, a game da matakan yaƙi da ta´adanci.

Wannan taro ya wakana a Dakar, babban birnin ƙasar Senegal bisa gayatar Majalisar Ɗinkin Dunia.

A cewar Birane Niang dake magana da yawun ministan shari´ar Senegal, ya zama wajibi ga ƙasashen Afrika, su shiga tunanin samar da hanyoyin riga kafi, da kuma na murƙushe matsalar ta´adanci, wadda a halin yanzu ta zama ruwan dare gama dunia.

Wannan matsala a cewar jami´in, na tafia kafaɗa da kafaɗa tare da sapara miyagun ƙwayoyi da makamai.

Sanarwar ƙarshen taron, ta nunar da cewa, ƙasashen yankunan yammaci da tsakiyar Afrika, sun cimma daidaito, ta fannin masanyar husa´o´i da bayyanai, wanda za su taimaka masu, su fuskanci yan ta´ada.