1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kare muhalli a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia

December 3, 2007
https://p.dw.com/p/CWK1

Samar da yarjejeniyar da zata maye gurbin ta birnin Kyoto wadda tanadi rage fid da hayaƙi mai ɗumama yanayi shi ne muhimmin batun da mahalarta taron na Bali ke mayar da hankali kai. Sama da mutane dubu ɗaya da suka haɗa da ´yan siyasa da masana daga ko-ina cikin duniya zasu shafe makonni biyu suna tattaunawa akan matakan da za´a ɗauka na dakatar da sauyin yanayi.

A shekara ta 2012 yarjejeniyar Kyoto zata ƙare aiki to amma ba mai tsammanin cewa taron na Bali zai samar da sabbin ƙa´idoji don ƙayyade yawan hayaƙin mai ɗumama doron ƙasa a duniya baki ɗaya. Izuwa shekara ta 2009 ake sa ran cimma wata sabuwar yarjejeniya bisa wannan manufa, inji shugaban hukumar kula da yanayi na Majalisr Ɗinkin Duniya Yvo de Boer a jawabin buɗe taron na Bali.

“A dangane da abubuwan da muka ci karo da su a shekarun baya, mun san cewa za a fuskanci matsaloli a taruka masu muhimmanci irin wannan. Ina da kyakkyawan fata cewa taron na Bali zai samar da madogara ta cimma wata yarjejeniya. Ina da tabbacin cewa tawagogin na masana kimiyya zasu magance wannan ƙalubale da ke gaban mu.”

Ƙungiyar tarayyar Turai na mai ra´ayin cewa kamata ya yi ƙasashe masu ci-gaban masana´antu su rag yawan gurɓataccen gas da suke fitarwa da kashi 30 cikin 100 kafin shekara ta 2020 idan aka kwatanta da yawansa na shekarar 1990. Sai dai kasar Amirka wadda ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar Kyoto ba, ta na ci-gaba da yin taurin kunne tana mai cewa dole ne a tilastawa ƙasashe dake samun matsakaicin ci-gaban masana´antu kamar China da Indiya da su kara ɗaukar matakan kare muhalli.

Ministan kare muhalli na Indonesi wanda ke shugabantar taron na Bali, Rachmet Witoelar ya yi nuni da cewa sauyin yanayi wani muhimmin batu ne ga makomar bil Adama.

“Ina kira ga dukkan mahalarta wannan taro da su ɗauki wannan batu da muhimmanci. Ya zama wajibi mu yi amfani da ƙa´idojin ƙudurin kare muhalli da muke da shi yanzu a matsayin ginshiƙin cimma sabuwar yarjejeniya da zata samu amincewar kowa.”

Masu fafatukar kare kewayen dan Adam sun yi kira ga wakilan ƙasashen dake halartar taron a tsibirin Bali da su samar da kwararan matakan dakatar da matsalar ta sauyin yanayi. Gabriela von Goerne masaniya a batutuwan kare muhalli a Jamus ta ce yanzu lokaci yayi da ya zama wajibi a rage dumamar yanayi da akalla mataki biyu a ma´aunin celsius.

“Tasirin da sauyin yanayin ke yi ba kadan ba ne. A hannu daya dole ne kasashe masu arzikin masana´antu su rage yawan gurbataccen hayaƙi da suke fitarwa sannan a daya hannu a gano hanyoyin taimakawa kasashe masu tasowa a koƙarin dakile matsalar nan ta lalata dazuzzuka.”