1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasa da kasa a Jordan kan Gabas Ta tsakiya.

Mahmud Yaya Azare
December 13, 2024

Ministocin harkokin waje na manyan kasashen duniya na taro a birnin Aqabah na kasar Jordan don duba halin da ake ciki a Syria kasa da mako guda bayan faduwar gwamnatin Bashar al Assad

https://p.dw.com/p/4o86D
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony BlinkenHoto: Virginia Mayo/AP Photo/picture alliance

Taron da ke zuwa a daidai lokacin da ake samun alamun samun gagarumin sauyi a yanayin siyasa da diflomasiyya a yankin Gabas Ta Tsakiya, bayan faduwar gwamnatin Assad da raguwar tasirin da Iran ke da shi, ya jawo samun fargaba biyu a yankin, wato samun kafuwar gwamnatin masu tsananin kishin Islama a Syria da karin karfin gwamnatin Yahudawa masu matsananancin ra'ayi da ke kokarin fadada iko da fadin kasarta a yankin, kamar yadda ministan harkokin wajen Jordan, Assafady ke fadi.

‘Dukkaninmu da muka hadu a nan fatanmu shine dakatar da yaki a wannan yankin namu nan take ba tare da gindaya wasu sharuda ba. Mun kuma yi amannar cewa hakan mai yiwuwa ne, idan da gaske za mu yi amfani da tasirinmu kan kawayenmu. Akwai bukatar Amurka ta dawo daga rakiyar da ta ke yi wa Isra'ila ido rufe. Babu wani dalilin da zai sanya Isra'ila ci gaba da kai wa Gaza da siriya hare haren cin zali domin yin hakan ne ke kara jawo gaba da tashe tashen hankula a yankinmu.”

Ministan harkokin wajen Jordan da wasu ministocin wajren kasashen Larabawa
Ministan harkokin wajen Jordan da wasu ministocin wajren kasashen LarabawaHoto: Reuters/M. Hamed

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da masu shiga tsakani don kawo karshen yaki a Gaza ke sanar da cewa, suna daf da cimma matsayar karshe kan yarjejeniyar dakatar da yaki da musayen fursinoni a tsakanin Isra'ila da Hamas, lamarin da ya sanya sakataren Amurka a yayin taron na Jodan ya ce suna son daukar duk matakan da suka wajaba don ganin rikicin Syria bai yi mummunan tasiri ga yunkurin dakatar da yaki a Gazan ba:

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Syria Geir Pedersen
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Syria Geir PedersenHoto: Mehmet Serkan Şafak/Andalou/picture alliance

"A yanzu mun dukufa wajen ganin an sami daidaituwar lamura a Syria ne. Muna fatan dukkanin kasashen da ke makwabtaka da kasar za su ba da hadin kai wajen cimma kodurorin kasa da kasa na tabbatar da Syria bata zama sansanin azabatar da jama'a ko mulkin kama karya da danniya kamar yadda take a lokacin Assad ba, kamar yadda muke fatan ba za a bar mulkin yan IS ya bulla a kasar ba.”

Wakilin kasar Turkiya a taron, Oglo Muhsin, kira ya yi ga kasashen duniya da su fito karara su yi tofin Allah tsine ga matakin da Isra'ila ke dauka na ragrgaza 80% na makaman rundunar sojin Syria, duk kuwa da cewa, kasar ta Syria bata taba kai wa Isra'ila wani harin cin zali ko neman ta da fitana ba, duk kuwa da mamaye Tuddan Golan mallakin Syria da Isra'ila ta yi tun kusan shekaru 60 din da suka gabata.

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa yayin taron su a Jordan
Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa yayin taron su a JordanHoto: AP

A yayin da kasar Masar ke cewa, Fadada yankunan mamayar da Isra'ila ta yi cikin Siriya wata mummunar aniya ce ta neman kara jefa yankin cikin wani sabon yaki, a daidai lokacin da ake jiran sabuwar gwamnatin da za a kafa a kasar ta Siriya.

Shi kuwa mukaddashin sakataren Majalisar Dinkin Duniya a taron Terry Jeprey Clansce, kira ya yi da a gaggauta ganin yadda za a yaukaka agajin da Syria ke bukata, tare da ba wa bangaren agaji muhimmanci, yana mai kira ga sabbin shugabanni kasar ta Syria da su bude kofofinsu ga kungiyoyin kasa da kasa don tabbatar da sa ido kan yadda kamun ludayin mulkinsu yake.