Taron kasa da kasa kan inganta yanayin muhalli
November 29, 2005Wakilan kasar Amurka a babban taro duniyan kan yanayin muhalli wanda ke gudana a birnin Montreal sun baiyana kudirin gwamnatin Amurka na rage gurbataccen hayakin masanaántu na Carbon dioxide dake gurbata muhalli. Wakilan sun kuma baiyana cewa ko da yake Amurka bata sanya hannu akan yarjejeniyar Kyoto ta kare muhalli ba, amma shugaban Amurkan George W Bush ya dauki batun kare muhallin da matukar muhimmaci. Taron wanda ke nazari a game da yadda zaá cimma nasarar rage hayaki mai guba na Carbon Dioxide da masanaántu ke fitarwa ya sami halartar wakilai fiye da 10,000 daga kasashe fiye da 180. Taron na tsawon makwanni biyu na duba hanyoyin samar da wani managarcin tsari da zai maye gurbin yarjejeniyar Kyoto ta kare muhalli a karshen karewar waádin shekara ta 2012.