1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli na shugabannin Afirka da Turai

November 29, 2017

Fiye da shugabanni 80 na kasashen Afirka daTurai sun hallara a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire a wani mataki na hadin gwiwa da nufin kirkiro guraben ayyuka da tabbatar da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/2oU94
EU-Afrika-Gipfel Bundeskanzlerin Angela Merkel und Alassane Ouattara
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Taron na kasashen nahiyoyin biyu na zuwa ne lokacin da kungiyar Tarayyar Turai ke ci gaba da alakanta makomarta ga nahiyar Afirka samakon tururuwar baki daga Afirkan zuwa Turai da kuma hare-hare irin na 'yan ta'adda dake mata brazana. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta jaddada muhimmancin kawo karshen safara da kuma bautar da al-umma da ake yi, tare da samar da hanyoyin da doka ta tanadar wajen shigowar 'yan Afirka zuwa Turai, hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da take shan matsin lamba a cikin gida dan magance turuwar da baki ke yi zuwa Jamus. 

Mittelmeer gerettete afrikanische Flüchtlinge
Daruruwan matasa daga Afirka na rasa rayukansu a tekuHoto: picture-alliance/AP/S. Diab

Shi ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke halartar taron ya  nuna damuwarsa dangane da yadda ake safarar 'yan nahiyar a wani lamari da ya ce kamar cinikin Akuyoyi.Taron ya kara kaimi a kokarin samar da limi da inganta rayuwar matasa ta hanyar samar da ci gaba, don kawo karshen yadda 'yan Afirka ke jefa rayuwarsu cikin hadari wajen tsallaka teku don neman ingattacciyar rayuwa a Turai. Kimanin 'yan Afirka 3000 ne ke bacewa ko mutuwa a duk shekara a Tekun Baharmaliya  

EU-Afrika-Gipfel in Abidjan
Bikin bude taron kasashen Afirka da TuraiHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Kungiyar Tarayyar Turai na fatan tallafin da za ta bayar ga kasashen zai iya rage yawaitar kwararar matasa ta cikin Sahara da tekun Baharmaliya zuwa Turai. Shugabannin kasashen Faransa da Beljiyam da kuma Luxembourg wadanda dukkannin su matasa ne 'yan kasa da shekaru 40 na kokarin nesanta kansu daga mulkin mulaka'un da kasashen Turan suka yi wa nahiyar ta Afirka inda suke alkawarin tallafawa Afirka wajen samar da ci gaba kamar yadda Charles Michel, Firaministan kasar Belgian ya sheda.

Kungiyar Tarayyar Turai  EU ta ware biliyoyin kudi na Euro don bunkasa tattalin arzikin Afirka da kuma karfafa hadin kai da kasashen nahiyar wajen dakile matsalar 'yan ta'adda. Abin jira a gani shi ne ko taron na kasashen Turan da Afirka zai taimaka wajen kawo karshen matsalolin da nahiyoyin biyu ke fukanta musamman ma nahiyar Afirka da ke zama ta baya ga dangi.