1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kungiyar AU ya gaza zaben shugaba

Zahraddeen Lawan/ YBJuly 18, 2016

An dai dage maye gurbin Nkosazana Dlamini Zuma har sai zuwa watan Janairu na shekarar 2017 inda za a zabi sabon shugaban Hukumar AU.

https://p.dw.com/p/1JR29
Ruanda AU-Gipfel in Kigali
Malarta taron AU a KigaliHoto: Getty Images/AFP/C. Ndegeya

Taron shugabanni daga kasashen Afirka da aka yi a birnin Kigali na kasar Ruwanda a ranar Litinin din nan ya gaza wajen zaben sabon shugaban hukumar a daidai lokacin da wa'adin Shugaba Nkosazana Dlamini-Zuma ke cika.

Wannan gaza cimma matsaya wajen zaben wanda zai gaji Zuma alamu ne na irin rikici da ke kwance a kasa a wannan kungiya. Za dai a yi zaben a taron koli da kungiyar za ta sake zama ne anan gaba a cewar Jacob Enoh Eben da ke magana da yawun Dlamini-Zuma. Babu dai dan takara daya cikin uku da ya samu yawan kuri'u kashi biyu cikin uku na kuri'un da aka kada cikin sirri.

Kafin zaben dai wasu kasashen na korafin cewa cikin 'yan takarar shugabancin hukumar ta Kungiyar Tarayyar Afirka daga kasashen Botswana da Equatorial-Guinea and Yuganda a wannan karo ba su da kwarewar da ta kamata su jagoranci hukumar, hakan dai ya sanya kasashe 28 daga cikin 54 na kungiyar ficewa a zagayen karshe na zaben abin da ya sanya dage zaben da kara wa'adin Zuma.

Ruanda Idriss Deby und Paul Kagame stellen neuen Reisepass vor
Shugaba Kagame da Debby na daga sabon fasfo na kasashen AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/A. Twahirwa

A taron an cimma matsaya ta samar da fasfo na bai daya da mambobin kungiyar za su amfana.

A lokacin taron shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka, Idriss Deby, ya ce ba zai yiwu a zuba ido ana kashe jama'a ba, tilas magoya bayan shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar a Sudan ta Kudu su mutunta yarjejeniya zaman lafiyar da aka cimma a watan Agustan 2015:

"Abin da ya faru a Sudan ta Kudu a jajiberin wannan taro namu na kara tunatar da mu mahimmanci tsaida dokokin bai daya wadanda suka dace da kasashenmu domin samar da hanyoyi na tinkarar ringingimun da kan iya barkewa a nahiyarmu".

Taron na kungiyar kasashen Afirka ya kuma amince, a yi amfani da kudaden harajin shigo da kayayyaki, inda ake son tara Dala biliyan daya da miliyan dubu dari biyu, don a rage dogaro da babban Bankin Duniya wanda shi ke samar da kudi kaso mafi tsoka wajen aiwatar da ayyuka a nahiyar Afirka.

Ruanda AU-Gipfel in Kigali
Mahalarta taron Kigali na darawaHoto: Getty Images/AFP/C. Ndegeya

Mai masaukin baki, shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, tun a ranar farko a jawabin sa na bude taron ya ce sun taru anan don su tattauna mahimman batutuwa da suka shafi nahiyar ta Afirka:

"Batun mutunta 'ya'ya mata shi ma babban batu ne da ke bukatar kulawa, kazalika tilas mu hada kai, mu samar da kudaden da za`a tafiyar da kungiyar AU."

Nkosazana Dlamini Zuma, wadda ke zama shugabar hukumar Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi sharhinta kamar haka:

“Mun tattauna yadda za'a kawo karshen rikici a Afrika, da kuma batun kawar da gwagwarmaya da makamai a nahiyar, mun amince mu kawar da fadace-fadace.