Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72
September 19, 2017Talla
A cikin shugabanin da za su halarci taron na bana akwai shugaba Donald Trump na Amurka da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron wanda shi ne karon farko da shugabanin biyu za su halarci taron bayan soma jan ragamar mulkin kasashensu. Gwajin makamin nukiliya da Koriya ta Arewa ke cigaba da yi da halin da Musulmi 'yan kabilar Rohingya ke ciki da batun yaduwar ayyukan ta'addanci da dumamar yanayi su za su mamaye taron na bana wanda shi ne karo na 72. Taron na kwanaki shida da zai gudana a birnin New York na kasar Amurka zai soma ne da jawabi daga bakin babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.