1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Mali ya dauki hankalin jaridu a Jamus

Mohammad Nasiru Awal
March 31, 2017

Taron da aka fara a ranar Litinin kuma ana sa ran kammala shi a wannan Lahadi ya na samun halartar wakilai kimanin 300 wadanda ke musayar ra'ayoyi.

https://p.dw.com/p/2aTQd
Präsidentschaftswahl Mali Bamako Ibrahim Boubacar Keita Politik Afrika Spitzenkandidat
Hoto: Katrin Gänsler

A wannan makon za mu fara sharhi da labaran jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Mali a daidai lokacin da aka bude zaman babban taron sasantawa.Ta ce babu kyakkyawar alamar samun nasarar taron domin tun ba a kai ko-ina ba kungiyoyin Abzinawa sun kaurace wa taron da aka shirya da nufin samo bakin zaren magance matsalolin yankin Arewacin Mali. Taron da aka fara a ranar Litinin kuma ana sa ran kammala shi a wannan Lahadi ya na samun halartar wakilai kimanin 300 wadanda ke musayar ra'ayoyi kan sasantawa da kuma hadin kan 'yan kasar ta Mali mai yawan al'umma miliyan 17.5. Jaridar ta ce kungiyoyin da suka kaurace wa taron sun yi korafin rashin kyakkyawan shiri ga taron, wanda kuma ke da nufin duba matsalolin arewacin kasar da har yanzu ake fama da rigingimun masu tsattsauran ra'ayi ga kuma yawan marasa aikin yi musamman tsakanin matasa.

Wanke Simone Gbagbo da ke zama matar tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da wata kotun birnin Abidjan ta yi ya dauki hankalin jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ma ta yi mamaki matuka dangane da wannan hukunci na wanke Simone Gbagbo daga aikata wani laifi a rikicin da ya biyo bayan zabenn kasar a 2010.

Jaridar ta ce a ranar Talata da ta gabata lauyan gwamnati ya nuna bukatar yanke wa Simone Gbagbo hukuncin daurin rai da rai a kurkuku. An gurfanar da ita a gaban kotu bisa zargin aikata laifi a kan dan Adam a lokacin tashin-tashina da ta auku a kasar daga shekarar 2010 zuwa 2011. Tuni dai kungiyoyin kare hakin dan Adam suka yi tir da hukuncin. Sai dai ba za a saki Simone Gbagbo ba, domin a 2015 wata kotu a birnin Abidjan ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 20 a kurkuku kan laifin yi wa kasa zagon kasa da shiga cikin wani bore da kuma tada zaune tsaye a cikin kasa. Majinta wato Laurent Gbagbo tun a karshen shekarar 2011 yake tsare a birnin The Hauge inda aka fara yi masa shari'a a bara. Ana zarginsa da laifin kashe mutane 325.

A karshe sai kasar Sudan ta Kudu a nan labarin inda har wayau dai jaridar Neue Zürche Zeitung ta buga labarin tana mai cewa dagangan ana hana mutane abinci saboda wasu muradu na siyasa.

Jaridar ta ce yawan kai hare-hare kan ma'aikatan agaji musamman ma masu kai kayan abinci a yankuna masu fama da yunwa a Sudan ta Kudu lamari ne mai tada hankali. Abin damuwa ma dai shi ne wadannan hare-haren sun fi aukuwar ne a yankunan da ke karkashin ikon dakarun gwamnatin Shugaba Salva Kiir. Hakan ya sa ake kara zargin gwamnatin da amfani da matsalar yuwan a matsayin makami kan abokan gaba.