1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abuja: Shirin kafa rundunar ECOWAS

Uwais Abubakar Idris LM
December 12, 2024

Ministocin kula da harkokin kasashen waje da na tsaro na kasashen kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, sun gudanar da taro a Abuja.

https://p.dw.com/p/4o50p
ECOWAS | CEDEAO | Mali | Jamhuriyar Nijar | Burkina Faso
Kokarin shawo kan matsalar tsaro a kasashen ECOWAS ko CEDEAOHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Yayin taron ministocin kula da harkokin kasashen waje da na tsaro na kasashen kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO din dai, sun bukaci kara kaimi wajen yaki da ta'addanci da sasanta rigingimun siyasa da ake fuskanta a wasu kasashen kungiyar. Taron karkashin kwamitin tsaro da shiga tsakanin na kungiyar da ke kokari na samar da rundunar tsaro ta shirin ko-ta-kwana a tsakanin, ya mayar da hankali ne a kan muhimmman batutuwa guda biyu da suka fi daukar hankali wato na dabarar da za su yi wajen bullowa barazanar da ayyukan ta'adanci ke ci gaba da yi da kuma rigigimu na siyasa da wasu kasashen kungiyar suka afka da ya haifar da 'yan gudun hijira. Taron dai ya zo a kan gaba, domin kuwa an gudanar da shi ne dai dai lokacin da ake kawo karshen shirye-shiryen da kungiyar ta yi na shawo kan matsaloli na aiyyukan ta'adanci a yankin da ta zama tamkar wutar daji da ta watsu zuwa kasashe da dama.

ECOWAS | CEDEAO | Mali | Jamhuriyar Nijar | Burkina Faso
Assimi Goita na Mali da Janar Abdourahamane Tiani na Nijar da Kyaftin Ibrahim Traore na Burkina FasoHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta dade tana shirin samar da rundunar tsaro ta shirin ko-ta-kwana, wanda tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso ake kai kawo kansa. Har yanzu kungiyar ba ta fitar da rai ba wajen amfani da lalama domin maido da kasashen da suka fice daga cikinta, saboda dawo da sojojin da suka kifar da dimukurdiyya zuwa cikinta. Kokarin da kasashen ke yi dai ya samu tagomashi daga Majalisar Dinkin Duniya, inda jakadan sakatare janar na majalisar a kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO da yankin Sahel Leonardo Simao ya bayyana cewa za ta ci gaba da taimakawa domin samar da zaman lafiya da bunkasa dimukurdiyya da mulki na gari da kyautata zamantakewa ta hanyar mayar da hankali a kan karfafa tattalin arzikin mata da matasa. Wannan shi ne karo na 54 da ake gudanar da wannan taro, kuma duk matsayar da suka cimma game da kudin da ake bukata da ma kasashen da za su bayar da sojoji a kan fara aikin rundunar shirin ko ta kwanan za a gabatar da su ne a gaban shugabanin kungiyar da zasu yi taro a karshen mako a Abujar.