Taron OPEC a Saudiyya
November 18, 2007Shugaba Hugo Chavez na ƙasar Venezuela,yayi gargaɗin cewar farashin gangan mai zai ninka zuwa dalan Amurka 200,idan har Amurka ta kaiwa Iran ko kuma Venezuela harin soji.Yayi wannan furucin ne ayayinda yake jawabi wajen buɗe taron kungiyar kasashe masu alobarkatun man petur na OPEC a birnin Riyadh ɗin ƙasar Saudi Arabia a jiya asabar,a yanzu haka dai farashin ɗanyen mai ya kusan kai dala 100 a kasuwanni.
Adangane da wannan takaddama na kasar Iran dai,ministan kula da harkokin ketare na Jamus Frank Walter Steinmeir cewa yayi,zamu tattauna wannan matsala ta a taron ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar turai a gobe litinin,kuma daga cikin muhimman batutuwa dake da akwai yanzu,shine dole muyi jiran sakamakon irin haɗin kai da Iran zata bawa hukumar binciken makamai ta majalisar ɗunkin duniya,wanda zaa gabatar.Bayan nan ne zamu san mataki na gaba