Taron sasanta bangarorin Sudan ta Kudu ya ci tura
August 18, 2015Taron sasanta bangarorin kasar Sudan ta Kudu masu gaba da juna da ya gudana a jiya Litanin a birnin Adis Ababa ya watse baram baram wannan . Shugaba Salva Kiir wanda ke halarci zaman tattaunawar ne ya ki ya saka hannun akan takardar yarjejeniyar zaman lafiyar wacce wakilin jam'iyyar SPLM da ke milki a Sudan ta Kudun da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar kana madugun 'yan tawayen kasar wato Riek Machar suka saka wa hannu.
Hukumomin Sudan ta Kudin sun ki su saka hannu a kan yarjejeniyar ne domin shakkun da suka ce suna da a kan wani sashe na abunda ta kunsa. Sun ce suna bukatar su sake yin nazarinta kafin su bada na'am dinsu a kai. Shugaba Salva Kiir dai ya ce nan da kwanaki 15 masu zuwa zai sake dawo wa domin bayyana matsayin gwamnatinsa a kan wannan yarjejeniya.
A Litanin din jiya dai ne wa'adin da manyan kasashen duniya suka bai wa bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudun na su sasanta ko su fuskanci takunkumai daban daban ya ke kawo karshe.