1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sasanta rikicin Palasdinu a Paris

Gazali Abdou TasawaJune 3, 2016

A wannan Juma'ar ce a birnin Paris na kasar Faransa aka bude wani zaman taron kasashen duniya kan sake farfado da shirin sasanta rikicin Isra'ila da Palasdinawa.

https://p.dw.com/p/1J067
Frankreich Internationale Nahost-Friedenskonferenz
Hoto: Reuters/S. de Sakutin

Taron dai shi ne na farko a cikin shekaru goman da suka gabata, sai dai kuma a wannan karon ya samu halartar ministoci da wakilan gwamnatocin kasashe kimanin 30 na Turai da na Larabawa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyara Turai ta EU zai wakana ne ba tare da wakilan bangarorin da batun ya shafa ba wato isra'ila da Plasdinu wadanda suka kaurace masa.

A jajibirin wannan taro dai ministan harakokin wajen Isra'ila ya ce ba su goyan bayan shi, domin a cewarsa duk wani yunkuri na neman sulhunta Palasdinwa da Isra'ila ta hanyar wasu masu shiga tsakani ba zai taba yin nasara ba, sai in ya zamo bangarorin biyu ne da kansu suka amince su zauna gaba da gaba su yi magana da samun daidaito tsakaninsu.