Taron Senegal a game da massasara tsintsaye
February 22, 2006A dangane da ci gaba da yaɗuwar cutar massara tsintsinya a Tarraya Nigeria, da ke barazanar ,ɓulla a sauran ƙasashen yammacin Afrika, ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yankin, wato Ecowas ko kuma, Cedeao, ta kiri wani taro a birnin Dakar na ƙasar Senegal.
Taron na yini 2, da a ka buɗa yau, ya samu halartar ƙurraru, ta fannin kiwon lahiar dabbobi, da su ka hito daga ƙasashen yammacin Afrika, da kuma na ƙungiyar Gamayya Tuari, da hukumar kiwon lahia, ta Majalisar Ɗinki Dunia, da FAO.
A jawabin buɗe taron, shugaban ƙasar Senegal Abdoulahi Wade, ya shawarci ƙasashen, da su yi tunani a kan hayoyin haɗa ƙarfi da ƙarfe, da kuma masanyar husa´o´i da bayanai tsakanin ƙasashe membobin Ecowas, domin murƙushe cutar murra tsintsaye kamin ta zama gagarabadau.
Sannan shugaban ƙasar Senegal ya shawarci girka wata cibiyar hadin gwiwa, tsakani ƙasashen ECOWAS,wace a cikin ta, za a iya binciken, gano ko tsintsaye sun kamu da wannan cutar ta zamani.
A halin yanzu, dukkan ƙasashen Afrika, na gudanar da binciken a nahiyar turai.
Wannan cibiyar bincike, a cewar Abdulahi Wade, zata buƙaci kuɗade kimanin Euro million ɗaya.
Taron na birnin Dakar, na gudana yan kwanaki kaɗan bayan bullar cutar murra tsintsaye a taraya Nigeria.
A yayin da ya yi nasa jawabi, mataimakin sakataran zartaswa, na kungiyar Ecowas, Monisaye Olusola Adfobali, yace bayyanan da ke issowa daga taraya Nigeria a dangane da batun murra tsintsaye, na da tayar da hankulla, a game da haka, wajibi ne a dauki matakan riga kafi ciki gaggawa a faɗin yammacin Afrika, da ma nahiyar baki ɗaya.
A wata sanarwar da ta hiddo yau, a birnin Roma, na ƙasar Italia, hukumar kulla da abinci ta Majalisar Dinkin Dunia wato FAO, ta ce gaggawar yaɗuwar mura tsintsaye a Nigeria, na buƙatar ɗaukar mattaka ƙwaƙƙwara.
Ɗaya daga wannan matakai ,inji daraktan hukumar kiwon lahiyar dabbobi ta Majalisar Ɗinkin Dunia, sun haɗa da larwan shigi da ficcin dukan tsintsayen daji ,da kuma hallaka dukkan wanda a ka tabbatar sun kamu da cutar.
A kan haka, cilas, a hada harfi tsakanin ƙasashe daban daban, kazalika ƙungiyoyi masu zaman kansu da ƙasashen masu hanu da shuni su bada tallafi mai tsoka.
Gobe idan Allah ya kai mu za a kammlla wannan taro, tare da bayyana sanarwa, a kan shawara da a ka tsaida.