Taron yaki da ta'addanci a Afirka a Nairobi
July 10, 2019Talla
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana hakan ne a wannan Laraba a jawabin bude babban taron yaki da ta'addanci a Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya inda ya ce wannan matsala ta faro daga kasar Mali ta yadu zuwa kasashen Nijar da burkina Faso, da kuma sannu a hankali ke yaduwa zuwa kasashen Ghana da Togo da Cote d'Ivoire.
Sai dai Guterres a shirye yake ya kawo goyon bayansa ga duk wani shiri da shugabannin nahiyar za su fito da shi na yakar ta'addanci a nahiyar baki daya. Guterres ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ya kasa sanya kungiyar ta G5 Sahel a karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda kasashe mambobin kungiyar suka bukata sau tari.