1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron 'yan jarida na duniya na DW

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 23, 2022

Tashar DW ta sake shirya taron 'yan jaridu na duniya da ta saba shiryawa duk shekara, inda a karon farko cikin shekaru biyu taron ya kasance na ido da ido.

https://p.dw.com/p/4D9fq
GMF 2022 | Taron 'Yan Jaridu na Duniya
Taron 'yan jaridu na duniya ido da ido, bayan annobar coronaHoto: Ronka Oberhammer/DW

Taron na bana dai ya kasance karo na takwas da tashar ta DW ke shiryawa, kuma a wannan karon ya karbi bakuncin kimanin mutane 2,000 daga sassa dabam-dabam na duniya da suka hadar da 'yan jaridu da masu fafutuka. Tashar ta DW dai kan shiyar wannan taron ne, domin tattauna matsaloli kan halin da duniya ke ciki da kuma lalubo mafita. Makomar aikin jarida da kuma matasa, na cikin abin da ya dau hankali a kololuwar taron na bana.

Batun yadda ake kallon labaran da suka shafi sauyin yanayi a ciki da wajen dakin labarai a duniya da bayar da rahotanni kai tsaye a fagen daga da kuma batun mata a fasahar aikin jarida da na fasalta aikin jarida a zamani na gaba ma dai, na daga cikin manyan batutuwan da taron ya mayar da hankali. Akwai kuma batun kalubale a fannin aikin kirkira a Afirka  da sashen al'adu na DW ya jagoranta, wanda shi ma ya yi matukar daukar hankali. Batun yakin da ake fafatawa tsakanin rasha da Ukraine ma ba a barshi a baya ba, domin kuwa an tattauna a kansa.