1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Masu tarzomar sakamakon zabe na ci gaba da gudana

Abdoulaye Mamane Amadou
February 25, 2021

Masu zanga-zangar adawa da sakamakon zabe a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da nuna turjiya da arangama da jami'an tsaro da aka baza a ko ina don kwantar da tarzoma.

https://p.dw.com/p/3puFD
Weltspiegel 24.02.2021 | Niger | Polizeieinsatz nach Wahlprotesten
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Baya ga toshe wasu manyan hanyoyi a Yamai da kone-konen tayoyi, masu zanga-zangar sun kai farmaki kan gidan wani dan jarida mai zaman kansa, kuma wakilin gidan Rediyon Faransa RFI Moussa Kaka, inda suka farfasa gidan tare da kona wani bangare na gidan.

A baya dai madugun 'yan adawar kasar Mahamane Ousmane da ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben da kaso 50,3 cikin dari na adadin kuri'un da aka kada, sabanin zababben shugaban kasar Bazoum Mohamed, da hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda yayi nasara da kaso 55,75 cikin dari na adadin kuri'un da akada a yayin zaben na ranar Lahadi da tagabata.

Kawo yanzu kafafen sadarwa na sada zumunta na ci gaba da kasancewa a takaice, bayan da manyan biranen kasar suka fuskanci toshe kafafen intanet a wani yunkuri na takaita zanga-zanga.