Tashin farashi: Idan komai ya yi tsada
Komai na kara tsada! Da wuya ake ganin irin yanayin da Jamus ta tsinci kanta a ciki a 'yan watannin nan. Jama'a na fama da tsadar kaya. Za mu duba kayayyakin da abun ya fi shafa.
Makamashi na zama abu mawuyaci
Wannan babbar matsala tafi shafar farashin makamashi. Bincike ya nunar da karuwar farashinsa da wajen kaso 58 idan aka kwatanta da baya. Kuma babu alamun mafita daga wannan yanayi na rashin sanin tabbas. Nauyin da ya koma kan masana'antu da mabukatu.
Farashin dumama gida
Wajibi ne jama'a su shirya wa yanayin sanyi mai tsada da ke tafe, a cewar mahukunta: A watan Yunin da ya gabata farashin dumama gida ya hau da wajen kaso 89 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Yunin bara. Alkaluma sun ce Jamus ba ta taba fuskantar tsadar man dumama gida har ya kai lita daya centi 123 ba. Shekaru shida da suka gabata dai lita daya centi 49 ne kacal.
Masu motoci na cikin tasku
Wannan matsala ta kuma shafi man da motoci ke amfani da su: An sayar da man Diesel a kan farashin Euro2.14 a watan Maris-farashi mai tsada a tarihi. Tsadar farashin man fetur ya taimaka wajen tsadar kayyaki masu yawa da ake shigo da su daga ketare, tunda da Dala ake biya. Rangwamen farashin mai a yanzu ya taimaka, amma fa kafin karshen Augusta kadai.
Tsadar wutar lantarki
Har ila yau wutar lantarki na kara zama kayan alatu. Bisa ga kwatancen portal Verivox, farashin wutar lantarki ya karu da kashi 32 cikin 100. Matakai kamar soke abin da ake kira karin cajin EEG ya saukaka wa masu amfani da wutar na gajeren lokaci, amma a zahiri ana cinye rangwamen ta hanyar hauhawar farashin asali.
Kayayyaki a jibge, babu kudi a aljihu
Tashin farashin kayan ya kai ga shagunan kayan abinci-babban damuwa musamman ga marasa karfi. Gaba daya dai farashin kaya ya haura da wajen kaso 12.7 fiye da shekarar da ta gabata, a cewar ofishin kididdiga. Duk da cewar akwai alamun farashin zai sauka cikin watannin da ke tafe, har yanzu batu ne na "muna fata".
Karancin man Burodi (Bota)
Dole mutane su shirya wa cin burodi ba tare da bota ba nan gaba. Don yawancin samfuran man burodin na dauke da alamar farashin Euro uku. Yakin Ukraine ya shafi manoma masu kiwo saboda tsadar shigo da kayayyaki don ciyar da dabobbobi da noma. Saboda haka manoman na kara juyawa zuwa samfura masu rangwame.
Karancin man girki
Ba wai mai ne kadai ke karanci saboda yakin Ukraine ba: Kaso 65 cikin 100 na man girki na duniya na fitowa ne daga Ukraine da Rasha. Mamayen da Rasha ta yi, ya dakatar da jigilar man zuwa waje. Hakan ya jagoranci karanci da tsadar man girki. Daga watan Afrilu zuwa Mayu kadai, farashin ya karu da wajen kaso 23.2 daga cikin 100.
Idan babu fulawa babu burodi
Tashin farashin kayayyaki ya shafi fulawar alkama. Inda farashinsa ya karu daga centi 93 a farkon shera ta 2022 da wajen kaso 127 daga cikin 100 daga shekarar da ta gabata. Don haka ne ake saran karuwar farashin wasu kayayyakin abinci da ake yi da fulawa kamar burodi.
Ya yi sauki!
Shin da gaske komai ya yi tsada? A'a, an samu rangwamen tafiye-tafiyen dogon zango da jirgin kasa cikin Jamus, godiya ga tikitin Euro 9 na wucin gadi, a cewar ofishin Kididdiga na tarayya. Kazalika tsarin nan na "sabis na hadin kai na jigilar fasinja" ya zama mai rahusa.