An soke bikin tunawa da samun 'yancin Senegal
April 4, 2020Talla
Gwamnatin Senegal ta tabbatar da cewa za ta samu koma bayan tattalin arziki da kashi 3 cikin 100 a wanna shekara ta 2020 sakamakon matsalar annobar cutar numfashi ta Coronavirus wadda ke ci gaba da dagula lamura a duniya, inda aka kwatanta da bunkasa tattalin arziki na kashi 6.8 cikin 100 da kasar ya mkamata ta samu a cikin shekarar.
Shugaba Macky Sall na kasar ta Senegal ya bayyana haka kuma bangaren yawon bude na kasar zai fi samun matsala.
A wannan Asabar 4 ga watan Afrilu kasar ta Senegal da ke yankin yammacin Afirka ta cika shekara 60 da samun 'yanci daga Turawan mulki mallaka na Faransa, kuma an soke bukukuwan da aka saba albarkacin wannan rana saboda annobar cutar ta Coronavirus.