1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar EU da Turkiya kan 'yan gudun hijira

Yusuf BalaMarch 4, 2016

Gabanin ganawarsu da shugaba Erdogan, jami'in kungiyar EU Donald Tusk ya ce babu hikima ga masu son shiga Turai saboda dalilai na tattalin arziki su jawo matsala tsakanin kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/1I72s
Türkei Ankara Treffen Tusk Erdogan
Shugaba Erdogan da Donald TuskHoto: Getty Images/AFP/J. Skarzynski

A ranar Juma'an nan shugaban gamayyar kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk zai gana da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya. Wannan tattaunawa da za a yi a birinin Istanbul, na zama a mataki na karshe cikin rangadi da shugaban ke yi a yankin, baya ga tattaunawa da Girka da Slovenia kafin taron koli da za a yi tsakanin kasashen na Turai da Turkiya a birnin Brussels a mako mai zuwa.

Bayan tattaunawa a birnin Athens da Alexis Tsipras firaministan Girka a ranar Alhamis, mista Tusk ya ce babu hikima ga masu son shiga Turai saboda dalilai na tattalin arziki su sanya shirin shiga kasashen na bai daya karkashin tsarin Schengen ya shiga rudani. A cewar mista Tusk lokaci ya yi da Turkiya za ta sa himma.

"Mun amince cewa yawan 'yan gudun hijrar ya karu matuka dan haka dole a kara daukar matakai,Turkiya ita ya kamata ta dauki duk matakin da ya dace".