Tattaunawar farko tsakanin Kiir da Machar
May 8, 2014Wani babban jami'i na kungiyar kasashen gabacin Afirka, Tewolde Gebremeskel ya ce jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar ya sauka kasar Habasha wato Ethiopia inda zai tattauna da shugaban Suda ta Kudu Salva Kiir. Gebremeskel ya ce Machal ya isa a birnin Gambella na kasar Habasha inda a wannan Jumma'a za a gudanar da tattaunawar farko tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu tun bayan barkewar rikicin kasar a cikin watan Disamban bara. Rikicin dai da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, sannan wasu kimanin miliyan 1.3 sun tsere daga gidajensu. Ma'aikatan agaji sun nuna fargabar barkewar annobar matsananciyar yunwa idan ba a kawo karshen rikicin kuma mutane suka yi shuka ba.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman