Tattaunawar sulhu a tsakanin Isra'ila da Falasdinu
July 30, 2013Wakilan Isra'ila da na Falasdinu da ke kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin sassan biyu, sun isa birnin Washington na kasar Amirka, domin fara tattaunawar da ta samu cikas na tsawon shekaru ukku kenan. A jawabin da ya yi game da tattaunawar, shugaban Amirka Barak Obama, ya ce a shirye kasarsa take ta nuna goyon baya ga tsawon lokacin gudanar da shawarwarin, tare da burin samar da kasashe biyu na Isra'ila da Falasdinu da za su zauna daura da juna cikin zaman lafiya da lumana.
Tunda farko dai, sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, ya gabatar da sabon manzon Amirka na musamman a yankin Gabas Ta Tsakiya, Martin Indyk, domin taimakawa kokarin samar da zaman lafiyar. Indynk dai tsohon jakadan Amirka ne a Isra'ila - a karkarshin gwamnatin tsohon shugaban Amirka Bill Clinton, kuma a jawabinsa na farko, ya mika godiyarsa ga Kerry, game da aikin da Amirka ta bashi:
Ya ce " Tun tsawon shekaru 40 ne, na yi amannar cewar, za a iya cimma burin samar da zaman lafiya. A bisa wannan dalili ne, nake godiya a gareka da kuma shugaba Obama da kuka dora mini nauyin ganin hakan ya tabbata, ta yadda za a kai ga cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Falasdinu."
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu