Taƙaddamar Isra'ila da Falasɗinu
March 13, 2011Hukumar Falasɗinu ta yi kakkausar suka ga amincewar da hukumomin Isra'ila suka yi na gina ɗaruruwan sabbin gidaje a yankunan Yahudawa 'yan-kama wuri zauna dake Gaɓar Tekun Jodan. Babban mai shiga tsakani na ɓangaren Falasɗinawa a tattaunawar samar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya Saeb Erakat ya ce akwai buƙatar rukunin masu shiga tsakani a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa daya ƙunshi Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai da kuma Amirka su sanya baki domin hana Isra'ila ci gaba da aiwatar da wannan matakin.
A yau Lahadi ne gwamnatin Isra'ila ta ce majalisar ministocin ƙasar ta amince da samar da ɗaruruwan sabbin gidaje a huɗu daga cikin yankunan da Yahudawa 'yan-kama wuri zauna suke a Gaɓar Tekun Jordan. Yanke shawarar dai ta zone ƙasa-da-Sa'oi 24 bayan da aka daɓawa wasu matasa biyu da ƙananan yara uku wuƙa - har lahiya yayin da suke kwance akan gadajen su a yankin Itamar dake kusa da Nablus, abinda yasa 'yan-kama wuri zaunan suka cinna wuta akan wani gidan Ba -Falasɗine dake kusa da yankin. Majalisar Ɗinkin Duniya dai tace manufar Isra'ila ta faɗaɗa gine-ginen ne babban tarnaƙi ga sake komawa bisa teburin shawarar samar da zaman lafiya a yankin na Gabas Ta Tsakiya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala