Teku na lalata garin tarihi a Senegal
Babban birni mai ban sha'awa a bakin tekun Saint-Louis yana fuskantar hatsari mafi girma daga hawan teku fiye da ko'ina a Afirka. Arzikin gine-gine da abubuwan more rayuwa na gargajiya na bakin tekun bacewa.
Gabar ruwa a Senegal
Wannan ita ce tashar jiragen ruwa ta Saint-Louis a Senegal. An gina birnin a karni na 17 saboda yana bakin teku da gabar kogin Senegal, kuma shi ne babban birnin kasar Faransa ta yammacin Afirka har zuwa shekarar 1902. Amma a yanzu, kusancinsa da teku barazana ce. Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa birnin na cikin hatsarin tashin gwauron zabi na teku fiye da sauran kasashen Afirka.
Kayan tarihi na duniya ya gushe
Mouhamadou Moussa Gaye, malamin makaranta, na kallon Guet Ndar, gundumar Saint-Louis da wurin tarihi na UNESCO. Guet Ndar ya mamaye dogon tsibirin "Langue de Barbarie" da ke raba gabar kogin Senegal da budadden teku. Makarantar da Gaye yake koyarwa, da masallatai da gidaje da ke gabar teku, sun lalace sakamakon zaizayar ruwa a gabar tekun.
Makarantu sun ruguje
Kasancewar a matsayin cibiyar UNESCO ta Duniya ba ya nufin yanayin din-din din. A nan ko da mafi yawan kayan aikin jama'a na iya fadawa cikin ruwan teku. Daliban da suka saba zuwa makarantar da aka lalata, an mayar da su wasu makarantu uku a cikin birnin. Amma duk da haka lokacin da darasi ya kare, har yanzu suna zuwa wasa a cikin tsoffin ajujuwan da suka rushe.
Zaizayar kasa ta rusa gidaje
A shekarar 2003, hukumomi sun haka hanya ta "Langue de Barbarie" yarra ruwa zai iya fita daga cikin gandun daji da kuma daga Saint-Louis lokacin da kogin Senegal ya yi barazanar ambaliya. Amma yunkurinsu na kare birnin ya citura. Ruwa ya bi ta hanyoyi guda biyu, ya lalata magudanan ruwan inda ta cinye mita 800 na gabar tekun Guet Ndar, da kauyukan da ke makwabtaka da ita.
Wani kauyen da ya bace
Ahmet Sene Diagne yana zama a irin wannan kauyen. Yanzu, yayin da yake kewaya ruwa a bakin teku daga Saint-Louis a cikin "kwale-kwale" tare da dansa, ya tuna yadda ya je zauren gari don gargadi game da tono magudanar ruwa, amma jami'ai ba su saurare shi ba. Sun ce in nuna takardar shaidar difloma, amma ba ni da ita, ina zaune a daji.
Babu makomar kamun kifi
Yanzu, duk abin da ake iya gani na kauyen Diagne shine kututturen bishiyar da ta taba tsayawa a tsakiyar fili - itacen da Diagne ya yi aure a karkashinsa. Iyalinsa ’yan kabilar Lebu ne, wadanda suka yi kamun kifi tun zamanin da. Yanzu an lalata al'ummominsu na bakin teku kuma Diagne ya ce babu makoma a kamun kifi. Yana fatan ingantaccen ilimi zai bai wa 'ya'yansa wasu zabin.
Tsohuwar bangon tekun mulkin mallaka
Latyr Fall, mataimakin magajin garin Saint-Louis, yana tsaye a kan tsohon bangon teku wanda ya taba kare birninsa. "An samar ne tun 1930 kuma Turawan mulkin mallaka na Faransa ne suka gina shi," in ji shi. Amma ba shi da tabbas cewa barazanar Saint-Louis ta kasance daga sauyin yanayi - kuma matakin teku ya tashi tun lokacin mulkin mallaka yana kira da a dauki sabbin matakan kare gabar teku.
Gina sabuwar badala mai karko
Gwamnatin Senegal na gina wani sabon badala mai tsawon kilomita 3da fadin mita 20 don kare Guet Ndar daga ci gaba da lalata gabar teku. Amma don daukar wannan katafaren gini, dole ne a rushe da yawa daga cikin sauran gidajen da ke bakin tekun da ke cikin hatsari don samun damar sabon aikin.
Jama'a sun nesanta kansu da gabar teku
Tare da tallafin Bankin Duniya da Faransa, an gina matsuguni da za a tsugunar da wadanda suka yi asarar gidajensu. da wandan suka g´muhallansu don ba da hanya. Kimanin kilomita 10 daga cikin gida a Diougop, mazaunan da suka rasa matsugunansu sun koka da cewa gidajen da suke ciki na daukar zafi da rana sannan ya yi da daddare, kuma babu isassun bandakuna.
Haihuwa daga ruwa
A yanzu Ahmet Sene Diagne yana zaune ne wani kauye mai suna Jel Mbaam, inda yake noma da sayar da amfanin gonarsa. A jikin bangon gidansa, ya rataye taswirar da ke nuna inda kauyensu yake kafin ruwa ya cinye. Har yanzu bai amince da matakan hukumomi na kare gabar tekun ba. "Ya kamata su shigar da mu a cikin shirin don mu ne ke zaune a nan, kuma daga ruwan nan aka haife mu," in ji shi.