Shawo kan matsalar tsaro a Tillaberi
August 19, 2021'Yan majalisar na Tillaberi, sun yi wannan kiran ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, inda suka yi bayani dangane da yadda matsalar tsaron ta nakasa yankin na Tillaberi, suna masu bayyana fasahohin da 'yan ta'addan ke amfani da su wajen kai hare-hare. Sanarwar ta kuma bayyana yadda matsalar tsaro ta nakasa harkar ilimi a jihar mai iyaka da Mali da kuma Burkina Faso, tare da zargin matakan da gwamnatin Nijar din ta dauka wajen tunkarar matsalar tsaron, sun kara jefa al'umma cikin halin ni 'yasu baya ga karya tattalin arzikin yankin.
Bayan bayani kan girman matsalar tsaro a yankin nasu, 'yan majalisar dokokin jihar ta Tillaberi sun fitar da jerin shawarwari zuwa ga gwamnatin ta Nijar ciki har da dage dokar hana yawo da babura a yankin. Daga karshe dai 'yan majalisar dokokin jihar ta Tillaberi, sun yi kira ga al'ummar jihar su kara bayar da hadin kai ga jami'an tsaro wajen ba su rahoton 'yan ta'adda a yankin, abin da suka ce hakan na zaman hanya mafi dacewa da za ta taimaka wa jami'an tsaron samun nasara ga abokan gabarsu.