Biden ya lashe zabe da magudi inji Trump
November 15, 2020Talla
Sai dai kuma ya nunar da cewa abokin hamayyarsa Joe Biden ya samu nasara ne saboda magudin da aka yi a zaben. Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce: "Ya lashe zaben ne saboda an tafka magudi."
Daga bisani ya sake wallafawa a shafin nasa na Twitter cewa, abin da ya wallafa da farko, ba yana nufin ya amince da sakamkon ba, yana mai cewa Biden ya samu nasara ne kawai a idon kafafen yada labarai da ke yada labaran karya.
Hakan dai na nuni da cewa har kawo yanzu Shugaba Trump na ci gaba da sukar sakamakon zaben, ba kuma tare da wata sahihiyar shaida da ke tabbatar da zarginsa ba.