Trump da shirin sasanta Isra'ila da Falasdinu
January 28, 2020Talla
Shugaban Amirka Donald Trump ya gabatar da shirinsa da aka dade ana jira na wanzar da zaman lafiya a tsakanin Israila da Falasdinawa yayin da ya karbi bakuncin Firamininsta Benjamin Netanyahu da jagoran adawa Benny Gantz a fadar White House.
Shirin ya bai wa Falasdinawa damammaki fiye da yadda aka yi tsammani. Wannnan dai abu ne da ake ganin ya kawo karshen rade radin cewa gwamnatin Shugaba Trump na shirin yin hakan ne ba tare da samun amincewar shugabannin Falasdinawa ba.
Trump ya bukaci Falasdinawan su amince da shirin, amma tuni suka ci alwashin yin fatali da shi. Amirka dai na kan bakarta na bai wa Isra'ila karfin ikon yankuna da dama na gabar yammacin kogin Jordan.