Dokar kwanaki 60 na hana baki shiga Amirka
April 22, 2020Talla
Shugaba Donald Trump ya ce matakin ba zai shafi ma'aikata da ke neman iznin shiga kasar ta Amirka a cikin wani dan takaitacen lokaci ba.
A yayin taronsa da ya saba yi da manema labarai a ko-wace rana, shugaban ya jaddada matsayinsa na daukar dokar, tare da nuna cewar akwai yiwuwar sake tsawaitata idan har bukatar hakan ta taso a wani yunkuri na kare aiyukan Amirkawa.
A yau dinnan ne ake saran zai rattaba hannu kan dokar.