Trump: Kasashen waje ka iya kai tsegumi
June 13, 2019Dan jarida mai gabatar da labarai a gidan talabijin na ABC George Stephanopolos ya tambayi Shugaba Trump ko da masu ba shi shawara za su iya karbar wasu bayanai na dan adawa daga Rasha ko Chaina ko wata kasa ta daban ko kuwa zai sanar da hukumar bincike ta FBI? A wannan karo sai Trump ya ce zai iya duk biyun.
"Ina tunanin mutum zai iya yin guda biyun, ina ga mutum zai so ya saurara, babu wani abu na rashin kyautawa a saurare idan wani ya kira daga wata kasa kamar Norway, cewa muna da wani bayani kan abokin hamayyarka, ina ga abin da zan so na ji ne."
Rawar dai da babban dan Trump ya taka a 2016 kan ganawa da lauya dan Rasha da ba shi bayanai da za a iya yarfen siyasa kan Hillary Clinton na daga cikin manyan abubuwa da lauya na musamman Robert Mueller da ya jagoranci binciken zargin hannun Rasha a murda zaben na Amirka ya duba.