Trump na neman dage zaben shugaban Amirka
July 30, 2020A karon farko, Shugaban Amirka Donald Trump ya nuna yiwuwar dage zaben shugaban kasa na 3 ga Nuwamba sakamakon yaduwar da annobar corona ke yi a kasar tamkar wutar daji. Cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tweeter, Trump ya ce zaben na fuskantar barazanar "magudi sakamakon zabe mafi karancin inganci da za a gudanar" a tarihin kasar Amirka, lamarin da ya ce zai iya zama "babban abin kunya ga kasar" idan aka samu karuwar yin zabe ta hanyar aikewa da wasiku a gidan waya. Sai dai shugaban bai bayar da wata kwakkwarar hujja game da tsoron da ya ji na magudi da kuste a zaben ba.
Ana ganin cewa Trump zai fuskanci cikas wajen dage zaben saboda doka ta riga ta kayyade lokacin da ya kamata a gudanar da shi. A halin yanzu dai, kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa Donald Trump na bayan abokin hamayyarsa Joe Biden na jam'iyyar Democrats a yawan wadanda za su kada masa kuri'a .