Gangamin kaddamar da takarar Donald Trump a wa'adi na biyu
June 19, 2019A gaban dandazon magoya banyansa da suka yi cincinrindo a birnin Orlando na Jihar Florida don gangamin kaddamar da shi dan takara, Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayyana anniyarsa ta zarcewa akan madafan iko, tare jaddada kamalun sa da yayi amfani da su ya yaki 'yan jam'iyyar adawa na Democrat da su a yayin yakin neman zaben kasar na shekarar 2016, inda ya yi kakkausar suka yana mai cewa zabar wani dan takarar jam'iyyar adawa ta demukrat tamkar sake sake maida mafarkin manufofin Amirkawa baya ne a 2020.
Shugaba Trump ya kuma tabo wasu muhimman ayyukan da gwamnatinsa ta yi na farfado da tattalin arzikin kasar, tare da bayyana matakinsa na karfafa danganta da kasar Isra'ila, sai dai Shugaba Trump ya caccaki yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da kasashen duniya da yanzu hakan ke cikin wani mawuyacin hali.
Masu sharhi dai na ganin tsayawar takarar ta Donald Trump ya kara fitowa da bukatarsa karara na cewar yana da burin yin wa'adin shekaru takwas ne kan madafan iko kamar yadda sauran tsoffin shuwagabannin da suka shude suka yi ciki har da Barack Obama, George W. Bush ko Bill Clinton.