Trump: NATO ta kara kudadenta na tsaro
July 11, 2018Talla
Shugaban Amirka Donald Trump ya yi kiran shugabannin kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO da su kara yawan kudaden da ake kashe wa harkoki na tsaro.
Yayin jawabin da ya gabatar lokacin taron jagororin kungiyar a Brussels babban birnin kasar Beljiyam, Mr Trump ya ce kamata ya yi a rika samar da kashi hudu cikin 100 na kudaden da ake samu daga kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida, akasin kashi biyu cikin 100 da suke samarwa a yanzun.
A share guda kuwa shugabannin na NATO sun amince da wasu muhimman batutuwa, musamman irin takun-sakar da ake samu tsakanin kasashen mambobin kungiyar.
Sun kuma amince da mika gayyata a hukumance ga kasar Macedonia da ta shigo cikin kawancen, bayan sasanta ta da aka yi da makwabciyarta wato kasar Girka.