1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai sake ganawa da Putin

Ramatu Garba Baba
July 20, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka ya mika wa takwaransa na Rasha Vladimir Putin goron gayata zuwa fadar White House a daidai lokacin da a ke ci gaba da sukansa bisa raunin da ya nuna a lokacin ganawa da Putin a Helsinki.

https://p.dw.com/p/31nW2
Finnland Helsinki PK Treffen Trump Putin
Hoto: Reuters/G. Dukin

Fadar Kremlin ba ta riga ta mayar da martani ba, sai dai zai kasance karon farko da wani shugaba na Rasha zai kai ziyara a fadar ta White House a kusan shekaru goma. Dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta yi tsami,  bisa adawa da Amirka ke yi da rawar da Rasha ke takawa a rikicin kasar Ukraine da Siriya da kuma zargin da a ke ma ta na yin kutse a zaben shugaban kasar Amirka na shekarar 2016.