1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya janye tallafi ga WHO

April 15, 2020

Shugaba Donald Trump na Amirka ya dakatar da samar da kudade ga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, a wannan lokacin da ake fama da annobar Corona yana mai zarginta da sakaci.

https://p.dw.com/p/3avBd
Washington Weißes Haus PK Coronavirus Trump
Hoto: AFP/M. Ngan

Shugaban na Amirka Donald Trump dai na zargin WHO ne da fifita kasar China a halin na annoba tare da zarginta da rufa-rufa da bayyanai kan hadarin wannan cuta tun da farko.

''Hukumar Lafiya ta Duniya ta ki bincika halin da ake ciki a Wuhan, musamman bayanai mau skaro da juna da aka samu daga gwamnatin China kan wannan cuta. Akwai sahihan bayanan da suka tabbatar da yaduwar cutar daga mutum zuwa mutum cikin watan Disamba, amma sai ta ki hakan nuna har cikin watan Janairu, ta kuma biye wa China da ke cewa ba haka abin yake ba.''

Shugaba Trump dai ya ce gwamnatinsa za ta yi bitar yadda hukumar take tafiyar da batun cutar ta Corona. 

A bara dai Amirkar ta bai wa WHO dala miliyan 400 a matsayin tallafinta.

Sai dai wasu masu nazarin al'amura sun karyata zargin Mr. Trump, inda suka nuna cewar hukumar ta yi wa duniya bayani kan cutar a watan na Disamba lokacin ta bulla a birnin Wuhan na Chinar.