Trump ya nisanta kansa da kutsen majalisa
January 14, 2021Da yake magana jim kadan bayan majalisar wakilan kasar ta sanar da tsige shi daga madafun iko, Trump ya ce babu wani wanda ya fi karfin doka a Amirka, yana mai ikirarin cewa masoyinsa na zahiri ba zai aikata irin wannan ba. Ya sha alwashin sai an hukunta duk mutanen da suka yi kutsen.
A jawabin da Trump din dai ya yi bai tabo batun tsige shi da majalisar wakilan kasar ta yi a ranar Laraba da daddare ba, amma tun da farko ya bayyana yunkurin a matsayin ci gaba da yi masa zagon kasa.
A yanzu za a mika kudurin tsige shi din zuwa majalisar dattawan kasar wace za ta tabbatar, sai dai kuma ana zullumin dattawan ba za su iya yin wannan aiki a cikin 'yan kwanakin da suka rage wa Trump ya kammala wa'adi sa ba. A makon gobe ne dai za a rantsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaban na Amirka.