Trump na yi wa makusantansa afuwa
December 24, 2020Mutane 23 sun hada da tsohon manajan yakin neman zabensa Paul Manafort wanda aka samu da badakalar kudi a cikin gagarumin binciken tsoma bakin Rasha a zaben Amirka na 2016, aka kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai. Sai Charles Kushner da aka yanke wa hukuncin zaman kaso na shekaru biyu bayan samun sa da kin biyan haraji. Kazalika akwai Roger Stone wanda aka kama sa da laifin shirga karya a rantsuwar da ya yi a gaban 'yan majalisa.
A yanzu Trump ya yi wa manyan mutane 49 afuwa daga hukuncin daurin da aka yanke musu a daidai lokacin da yake shirin sallama da madafun iko a wata mai kamawa. Sai dai irin wannan ba sabon abu bane a shugabancin Amirka, domin tsohon shugaban kasar Barack Obama ya yi wa daruruwan masu laifi afuwa a ranarsa ta karshe a fadar White House.