1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sanya hannu akan tallafin corona

Binta Aliyu Zurmi
December 28, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya saka hannu a kan kudirin tallafin annobar corona da 'yan majalisar wakilan Amirka suka amince da shi da nufin ceto kasar daga matsin tattalin arzikin da annobar corona ta jefa kasar.

https://p.dw.com/p/3nGv7
USA | Washington | Donald Trump Thanksgiving Videokonferenz
Hoto: Erin Schaff/Zuma Wire/Imago Images

Kimanin dala biliyan 900 ne kudirin ya kunsa wanda da dama daga cikin 'yan majalisun suka amince da shi.

Za a yi amfani da wadannan kudadde ne wajen taimaka wa kamfanoni da masana'antu da kuma wadanda suka rasa aiyukansu.

Amirka ce dai a sahun gaba a cikin kasashen da aka sami asarar rayukan jama'a da dama a sanadiyar cutar corona, mutum sama da miliyan goma sha takwas cutar ta kama a kasar wasu fiye da dubu dari uku suka rasu.