Trump ya yi barazanar kara haraji kan EU
December 20, 2024A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump yace ya sanar da kungiyar tarayyar Turai cewa dole ne su kara azama wajen cike gibin cinikayyarsu da Amurka ta hanyar kara yawan mai da iskar Gas da suke saye daga Amurka.
A bisa alkaluman kididdiga na Amurka, kungiyar tarayyar Turai ita ce kan gaba wajen sayen makamashi daga Amurka.
Tuni dai Trump ya yi alkawarin lafta haraji mai yawa a kan wasu kasashe uku da ke kan gaba wajen cinikayya da Amurka wadanda suka hada da Canada da Mexico da kuma China idan ya karbi ragamar mulki a ranar 20 ga watan Janairun 2025
Matakin dai ka iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya.
Jamus ita ce kan gaba a cikin kasashen Turai da ke safarar kaya zuwa Amurka galibi motoci da na'urori da kuma magunguna.