Trump ya yi watsi da tayin soke izinin mallakar bindiga
March 28, 2018Talla
A cikin wani sako da ya wallafa a wannan laraba a shafinsa na Tweeter, Shugaba Trump ya bayyana cewa har abada ba za a soke wannan kudiri ba. A jiya Talata ce alkali John Paul Stevens tsohon mamba a kotun kolin kasar ta Amirka ya yi kira ga Shugaba Trump da ya soke kudirin da ya bai wa Amirkawa izinin mallakar bindiga wanda karni biyu kenan ake cece-kuce da ma sabanin fahimta kansa.
Masu fafutukar kare 'yancin mallakar bindiga a kasar ta Amirka dai na kallon wannan kudiri na izinin mallakar bindigar a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci ga rayuwar Amirkawa.