Trump: za a hana 'yan Najeriya shiga Amirka
February 1, 2020Talla
Gwamnatin Amirka ta kebe ranar 22 ga wannan wata na Fabrairu a matsayin ranar da wannan tsari zai fara aiki kamar yadda hukumar shige da ficen kasar ta sanar. Wannan sabon tsari na zuwa ne gabanin zaben da kasar za ta gudanar a bana, shekaru uku bayan shugaba Trump ya haramta wa wasu kasashe shiga Amirka. Al'amrin da ya haifar da cece-kuce.
Tun bayan hawan sa mulki shugaban na Amirka ya tsaurara wa wasu kasashe da suka hada da kasashe 'yan rabbana ka wadata izinin shiga Amirka. sai da kasar Tantaniya ta mayar da martanin cewar Amirka ba ta sanar da ita a hukumance ba don haka ba ta da masaniya.