Amirka: Za a kai bakin haure a garuruwan adawa
April 13, 2019A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tweeter, Shugaba Trump ya ce ta la'akari da yadda 'yan jam'iyyar Democrates ke nuna adawa ga bukatarsa ta daukar sabbin dokoki na tsaurara matakan hana kwararar bakin haure zuwa kasar, ya soma nazarin yiwuwar aikawa da tarin bakin hauren da ake tsare da su zuwa biranen San Francisco ko Shicago wadanda suke bayar da mafaka da ma kariya ga tarin bakin haure da ke da zama a cikinsu, da kuma kim ba da hadin kai ga jami'an yaki da bakin haure a kasar.
A sakon nasa Shugaba Trump ya yi shguban cewa ya yi imanin wannan mataki nasa zai faranta wa jam'iyar adawar ta Democrate da rai matuka. Sai dai magadan garuruwa da dama daga cikin wadanda shugaba Trump ya yi barazanar aika masu da bakin hauren, sun mayar da martanin cewa a shirye suke su karbi duk wasu bakin hauren da zai aiko a cikin garuruwan nasu.