Tsadar burodi a Sudan ta dauki hankalin jaridu a Jamus
January 12, 2018Za mu fara sharhi da labarun jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan mako ta leka kasar Sudan tana mai cewa: Bore dangane da tsadar burodi a Sudan, inda al'umma a sassa dabam-dabam na kasar suka yi ta boren adawa da ninka farashin burodi har sau biyu, yayin da ita kuma gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir ta yi kokarin amfani da karfi don murkushe boren, amma ba ta yi nasara ba. Jaridar ta ce karin farashin burodi ya zo ne domin gwamnati ta sauya fasalin shigo da hatsi kasar ta kuma mayar da harkar hannun 'yan kasuwa masu zaman kansu. Burodi dai na zama wani abinci mai muhimmanci a Sudan wanda kuma ninka farashinsa ya fi shafar rayuwar yau da kullum ta talakawa a kasar. Jaridar ta ce bisa ga dukkan alamu tsadar farashin burodin na zama wani abin da karshen hakurin 'yan kasar har ya kai su da yin bore. Kasancewa dalibai da yawa na cikin masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa, hakan ya ba su damar nuna fushinsu da yadda ake tafiyar da mulkin kasar.
Bisa ga dukkan alamu murna ta koma ciki ga ‘yan adawar kasar Habasha a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung sannan sai ta ci gaba tana mai cewa.
A ranar Laraba ta makon jiya an ruwaito Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn na fada wa wani taron manema labari cewa gwamnati za ta sako dukkan firsinonin siyasa. Amma kwanaki kadan bayan wannan labari da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya suka yi maraba da shi, gwamnati ta musanta labarin da cewa an yi mata gurguwar fahimta. Ta ce a kasar ta Habasha babu firsinan siyasa balantana a yi maganar sakin dukkansu daga kurkuku. Amma gwamnatin ta ce za a yi wa wasu daga cikin jagororin ‘yan siyasa da aka kama afuwa. Kungiyar Amnesty International ta yi kiyasin cewa akwai ‘yan adawa kimanin 2000 a gidajen kurkukun kasar ta Habasha ko da yake babu wata kafa ta dabam da ta tabbatar da wadannan alkalumma.
A karshe sai jaridar Der Tagesspiegel wadda ta ce ana tababa dangane da matakin haramta cinikin hauren giwa da mahukunatan kasar China suka yi.
Jaridar ta ce mako guda ke nan da China ta haramta cinikin hauren giwa a kasar a wani mataki na ba da tata gudunmawa wajen kare giwaye da ke fuskantar barazanar gushewa musamman a nahiyar Afirka, inda ake farautarsu ta barauniyar hanya. Tun dai a 1989 aka haramta cinikin hauren giwa a duniya, amma ta ci gaba da ba wa 'yan kasarta izinin saye da sayar da hauren giwa a cikin iyakokin kasa. To sai dai ana nuna shakku da sabon matakin da Chinar ta dauka na haramta cinikin, inda masana suka ce tun a 2014 bukatar hauren giwa ta ragu a China, farashinsa kuma ya fadi, saboda haka matakin wata dabara ce ta sauya al'amura.