1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fara amfani da shirin tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 12, 2016

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu ta fara aiki wadda ake fata za ta kawo karshen sabon rikicin da ya barke tsakanin bangarori masu adawa da juna.

https://p.dw.com/p/1JNmJ
Südsudan Juba SPLA Rebellen
Hoto: Getty Images/AFP/S. Bol

Kuru ta lafa a Juba babban birnin Sudan ta Kudu sakamakon mutunta kiraye-kirayen tsagaita wuta da bangarorin da ke baiwa hamata suka yi. Kwanaki hudu dakarun Shugaban Salva Kiir da na 'yan tawayen da ke biyayya ga mataimakin shugaba Riek Machar suka shafe suna ba ta kashi, lamarin da ya jefa dubban mazauna Juba cikin kuncin rayuwa.

Babu ko da harbin bindiga daya ballatana na gurneti da aka ji a Juba babban birnin Sudan ta Kudu a wannan Talata. Sannan shaidu da kafofin watsa labaran kasar sun ruwaito cewa, sabanin kwanakin baya, jirage masu saukar ungula ba su yi shawagi a sarararin samaniyar birnin ba. Abin da ke nuna cewa kura ta lafa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Sudan ta kudu.

Südsudan Regierungstruppen - Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/A. Gonzalez Farran

Maimakon haka al'amura sun fara kankama. Alhali kwanaki uku a jere, kazamin fada ne aka gwabza tsakanin sojojin da ke biyayya ga Shugaban Salva Kiir da kuma mayakan mataimakinsa kuma tsohon dan tawaye Riek Machar.

Sai dai hukumar da ke kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa dangane da halin da 'yan Sudan ta Kudu da suka tsere wa matsugunansu ke ciki, kamar yadda kakakinta wannan hukuma Alessandra Velluci ta bayyana.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka rasa rayukan a wannan artabu ba. Amma dai bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu sun yi intifakin cewa daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a wannan sabon fada, da ya zo lokacin da kasar ke cika shekaru biyar da samun 'yancin kanta.

Südsudan Flüchtlinge suchen Schutz UN-Mission in Juba
Hoto: picture-alliance/dpa/UNMISS/E. Kanalstein

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna bacin rai dangane da mayar da bara bana da bangarorin da ba sa ga maciji da juna ke yi a Sudan ta Kudu. Jami'in ya nemi a kakaba wa kasar takunkumin hana shiga da makamai, tare da neman da a ladabtar da wadanda aka samu da hannu wajen rura wutar wannan sabon rikici. Hakazalika Ban ya yi kira a alkinta aikin sojojin kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu ta hanyar samar musu da jiragen yaki.

Wannan sabon fada na Sudan ta Kudu yana barazana ga yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Kiir da mataimakinsa Machar suka amince a ranar 26 ga watan Agusta na 2015. Lamarin da ke sa fargabar shiga cikin wani rikici.