1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta ya fara aiki Sudan

Usman Shehu Usman
April 25, 2023

'Yan kasar Sudan da baki mazauna kasar wadanda suka makale tsakanin fagagen yaki a kasar sun fara fecewa daga inda suka fake bayan samun lafawar harbe-habe tsakanin masu yaki da juna.

https://p.dw.com/p/4QYGf
Bildergalerie | Evakuierung von Ausländern aus dem Sudan
Yadda ake ta kwashe baki a SudanHoto: Laure-Anne MAUCORPS/Armee de l'air et de l'Espace/Etat-major des armees/REUTERS

Wanna ya samu ne biyo tsagaita wutan kwanaki uku da aka samu, inda dubban mutane suka fada tsakiyan yaki. An dai fara aiki da yarjejeniyar tsaigata wuta ta kwanki uku, wace kasashen Amirka da Saudiya suka jagoranci cimmawa. Kungiyoyin bada agaji sun sanar da cewa yanayin jinkai a kasar Sudan ya yi matukar muni fiye da yadda ake zato. Sama da kwanaki goma ana luguden wuta a biranen kasar ba kakkautawa, abin da ya jawo yakin ya shafi al’umma da yawa. Fadan dai ya fi muni ne a Khartoum babban birnin kasar da kuma Omdurman. Yanzu haka dai kasashen duniya na kai kawo don kwashe jama’arsu daga Sudan.