Tsagerun kungiyar Al-Shabaab sun kashe 'yan sanda a Kenya
March 2, 2018Talla
Sanarwar ta kara da cewar Jami'an tsaro na cigaba da bincike a halin yanzu,shi dai wannan hari na zuwa ne kwana daya bayan wasu masu rajin kare hakkin 'dan Adam sun zargi jami'an 'yan sandan kasar da kisan wadanda ake zargi da 'yan kungiyar Al-Shabaab ne da suka dawo daga kasar Somaliya a garin Mombasa.
Kungiyar ta'addanci ta Al-Shabaab na cigaba da kai hare hare gidajen shakatawa da ma'aikatun gwamnati a kasar Somaliya in da kungiyar ta samo asali,mummunan hari na karshe da kungiyar takai a kasar shine wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da 500 a shekarar da ta gabata.