RGB
April 20, 2021Talla
Mahukuntan Saudiya sun gabatar da sabbin dabarun tsaftace Ka'aba da farfajiyar Harami cikin karamin lokaci da kuma busar da shi, ba tare da an samu dogon tsaiko ga masu ibada ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Saudiya ya bayar da rahoton. A karon farko a tarihi an gudanar da aikin wanke dakin Ka’aba da farfajiyar masallacin harami mai tsarki a cikin lokaci mafi karanci, inda ma’aikatan da suke kula da tsaftar wurare masu tsarki su kimanin dubu hudu suka gudanar da aikin a cikin kasa da mintuna biyar suka kuma kamala.